Home Labaru Masu Kishi Da Rikon Amana Zan Zaba A Sabbin Ministoci – Buhari

Masu Kishi Da Rikon Amana Zan Zaba A Sabbin Ministoci – Buhari

635
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Duk da matsin lambar da shugaban kasa Muhammadu Buhari  ke fama da ita kan nada sabbin ministoci ya ce, ba zai taba yarda ya sake zabar wanda bai sani ba.

Shugaba Buhari, ya ce domin ya samu nasarar ci gaba da gudanar da ayyuka a zangon na sa karshe, sai wanda ya sani na hakika zai zaba a matsayin minista.

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a zaman tattaunawar sa da shugabannin majalisun dokoki, inda ya kara da cewa, sai wanda ya san shi da kishin kasa da kokarin tabbatar da ci gaba da rikon amanar al’umma zai zaba a matsayin minista .

Karanta Labaru masu Alaka: Kwararru Kuma Amintattu Kawai Zai Nada Ministoci

A zaman tattanawar wanda aka yi a Fadar shugaban kasa Buhari, yana fuskantar matsin lamba dangane da nada ministocin dan haka duk matsin lambar ba zai yi gaggawa ba, sai ya tabbatar da amintattun mutanen da zai zaba wadanda suke da kyakkyawar shaida ta rike amanar al’umma.

Yace ya san da dama daga cikin ‘yan majalisar sun zo taron ne da sa ran za su ji sunayen sabbin ministocin domin hankalin su ya kwanta, ya san da wannan kuma shi ma yana fuskantar matsin lamba  kan hakan.

Karanta Labaru Masau Alaka: Shugaba Buhari Ya Yi Wa Wasu Hafsoshin Soji Karin Girma

Shugaba Buhari, yace ma fi yawan ministocin da ya yi aiki da su a zango na farko bai san su ba, jam’iyya ce tare da wasu mutane suka turo da sunayen.