Home Labaru Ilimi Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 208 Don Bunkasa Makarantu – Bogoro

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 208 Don Bunkasa Makarantu – Bogoro

575
0
Farfesa Suleiman Bogoro, Shiugaban Hukumar Kula Da Manyan Makarantu Ta Nijeriya, TETFUND
Farfesa Suleiman Bogoro, Shiugaban Hukumar Kula Da Manyan Makarantu Ta Nijeriya, TETFUND

Gwamnatin trayya ta ware wa hukumar kula da manyan makarantu ta Nijeriya TETFUND kudi Naira miliyan dubu 208 domin kula tare da bunkasa manyan makarantun gwamnati a shekarar karatu ta 2019, wadanda suka hada da jami’o’i kwalejojin kimiyya da fasaha da na horar da malamai a fadin kasar nan.

Bayani ya fito daga shiugaban hukumar, Farfesa Suleiman Bogoro, a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a sha’anin manyan makarantun da za su ci gajiyar wadannan kudade da hukumar ta gudanar a tsakiyar mako, a babban birnin tarayya Abuja.

Karanta Labaru Masu Alaka: Gwamnatin Kebbi Ta Ce A Ba Dalibai 7,000 Damar Rubuta Jarabawa A Kwalejin Kimiyya

Farfesa Bogoro, ya yi karin haske dangane da yadda aka karkasa kudaden zuwa wadannan manyan makarantun, inda ya ce kowace jami’a da za ta ci gajiyar kudin, za ta samu Naira miliyan 826,  da dubu 684, da 392, yayin da kowace kwalejin kimiyya an ware mata Naira miliyan 566,  da dubu 701, da 842 sai kwalejojin horar da malamai da suka samu Naira miliyan 542, da dubu 226, da 346.

Bugu da kari kuma, ya ce a karkashin tallafin karatu na musamman wanda manyan makarantu 18 za su ci gajiyar sa a shiyoyi shida da ke fadin tarayyar Nijeriya, wadanda suka kunshi ware Naira miliyan dubu 3 ga jami’o’i shida, naira miliyan dubu daya ga kwalejojin kimiyya da wasu Naira miliyan dubu daya da aka ware wa kwalejojin horar da malamai a yankunan.

Leave a Reply