Home Labaru Mafita: Jonathan Ya Ce Sai An Yi Amfani Da Rahoton Taron Kasa...

Mafita: Jonathan Ya Ce Sai An Yi Amfani Da Rahoton Taron Kasa Na Shekara Ta 2014

265
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce lokaci ya yi da za a jingine bambance-bambancen siyasa a aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton taron kasa da aka gudanar a shekara ta 2014.

Ya ce gwamnatin sa ba ta samu ikon aiwatar da shawarwarin zaben ba ne saboda kurewar lokaci, duba da cewa daf da zaben shekara ta 2015 aka mika masa rahoton.

Jonathan ya bayyana haka ne, a wajen taron kaddamar da wani littafi mai shafuka 669 da fittacen dan siyasa Sanata Femi Okurounmu ya rubuta.

Goodluck Jonathan, ya ce za a magance mafi yawancin matsalolin da ke addabar Nijeriya idan aka aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton taron kasa na shekara ta 2014.

A karshe ya bukaci a sauya tsarin yadda ake nada Shugaban hukumar zabe ta kasa da sauran jami’an hukumar domin samun zabubbuka masu inganci.