Home Labaru Maslaha: Masarautar Kano Ta Ce Bata Gaba Da Gwamnatin Ganduje – Sarki...

Maslaha: Masarautar Kano Ta Ce Bata Gaba Da Gwamnatin Ganduje – Sarki Sanusi

870
0

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ce masarautar sa bata gaba da gwamnatin jihar Kano kamar yadda wasu ke hasashe.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi ga ‘yan majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Abdul’aziz Gafasa, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadar sa.

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II

Ya ce a shirye masarautar kano ta ke wajen gudanar da ayyuka ci-gaba a jihar a karkashin gwamnatin Ganduje, sannan Sunusi ya kara da cewa gwamnatin kano acikin shekaru biyu da suka gabata ta amince masa ta hanyar neman shawarwari a kan hanyoyin habbaka martabar kasuwanci a jihar.

Sarki Sunusi ya ce kasancewar sa cikin lamarin ya bude kafar da gwamnatin jihar ta kammala samar da abinda aka fi bukata wajen tabbatar da wannan sauyi a masana’antun jihar, sannan gwamnatin jihar ta yi amfani da rahoton da ya bada domin cimma wannan manufa. A karshe ya ce, ya zama wajibi ayi amfani da matsayin Kano na cibiyar kasuwancin a arewacin Nijeriya wajen samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a jihar dama sauran jihohin Nijeriya.