Majalisar Dinkin Duniya ta ce lalacewar kasar noma da karancin filin noma da ruwa ya haddasa matsalar tsaro a Nijeriya fiye da kungiyar Boko Haram.
Sakatare majalisar a kan harkokin yaki da zaizayar kasa Ibrahim Thiaw ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a lokacin da ke gudanar da taron ranar yaki da zaizayar kasa na duniya ta ya gudana a kasar Turkeya, sannan ya ce, dalilin rikicin shine gasa wajen neman ma’adanai.
Idan dai ba a manta ba, ana gudanar da bikin ranar yaki da zaizayar kasa ta duniya a ranar 17 na watan Yuni kowacce shekara, domin inganta yadda ake amfani da kasa domin amfanin ‘ya’ya da jikoki da za su zo a nan gaba.
Kamfanin dillanci labaran nijeriya NAN ya ruwaito cewa, gwamnatin kasar Turkey da Majalisar Dinkin Duniya ne suka dauki nauyin gudanar da wannan taro da aka gudanar a turkiya wanda ya samu hallartan ministoci 10.
Majalisar dinkin duniya ta ce, karuwar al’umma da bukatun su tare da dumamar yanayi da ragowar albarkatun kasa ne musababbin rikice-rikicen da suka janyo zubar da jinni a fadin duniya.