Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ma’aikatar Ƙwadago ta kafa kwamitin da zai duba daina amfani da ƙayyade shekarun neman aiki a Nijeriya, biyo bayan ƙudirin da Sanata Ibrahim Gobir ya gabatar.
Sanata Ibrahim Gobir, ya ce ‘yan Nijeriya da dama su na rage yawan shekarun su na haihuwa a ƙoƙarin su na shiga cikin rukunin waɗanda za a ɗauka aiki.
Ya ce duk lokacin da mutum ya san cewa ba za a ɗauke shi aiki ba to zai bi wasu hanyoyi da ba su dace ba, lamarin da ke janyo ƙaruwar aikata laifuffuka da kuma rashin tsaro a ƙasar nan.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya yi Allah-wadai da yadda ake nuna ma wasu masu neman aiki wariya saboda shekarun su,kuma babu laifin da su ka aikata da zai sa a nuna masu wariya.