Home Labaru Fyade; Ya Kamata A Fara Dandake Masu Aikata Laifin – Gbajabiamila

Fyade; Ya Kamata A Fara Dandake Masu Aikata Laifin – Gbajabiamila

219
0

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya bada shawarar a tsananta ukuba a kan masu fyade sakamakon yadda kararrakin fyade su ka yawaita kwanakin nan a fadin Nijeriya.

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila

Gbajabiamila, ya ce matsanancin hukuncin ka iya hadawa da yanke al’aurar duk wanda aka kama da laifin fyade.

Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar yaki da ayyukan fyade a ofishin sa da ke Abuja.

Ya ce lamarin fyade ya zama annoba a Nijeriya, kuma kafofin yada labarai su na da rawar takawa wajen yaki da ita, don haka ya kamata a maida hankali a kan lamarin fyade kamar yadda aka maida a kan Coronavirus.