Home Masar Ta Gindaya Sharuɗɗan Kwashe Ɗaliban Najeriya Ta Cikinta

Masar Ta Gindaya Sharuɗɗan Kwashe Ɗaliban Najeriya Ta Cikinta

Jakadan Nijeriya a Masar Nura Abba Rimi, ya Masar ta ce za ta yarda a kwashe ɗaliban Nijeriya da ke tsere wa faɗan da ake yi a Sudan ta ƙasar ta ne kawai idan Nijeriya ta cika wasu tsauraran sharuɗɗa.

Nijeriya dai ta na da sama da ɗalibai 500 da su ka maƙale a bakin iyakar ƙasar Masar, su na jiran izinin shiga domin kwaso su zuwa gida.

A baya dai ƙasar Habasha ta hana ɗaliban Nijeriya bi ta ƙasar ta domin tsere wa faɗan Sudan, lamarin da ya janyo suka daga ɓangarori da dama.

Ambasada Nura Abba Rimi, ya ce sharuɗɗan da ƙasar Masar ta gindaya wa Nijeriya sun hada da cewa, dole sai Nijeriya ta bayyana tsarin da ta yi na jiragen da za su sauka a ƙasar domin kwashe ɗaliban da kuma girman jiragen saman da za su yi jigilar.

A kuma tabbatar da cewa za a zarce da ɗaliban kai-tsaye daga bakin iyakar ƙasar zuwa filin jirgi da aka yarjemawa, da cikakken jerin sunayen mutanen da za a kwaso da lambar fasfon su na tafiye-tafiye da kuma cikakkun takardun tafiya, sanna jami’an gwamnatin Nijeriya su kasance a wuraren da za a kwaso ɗaliban, da kuma motocin safa da za su kwaso ɗaliban daga bakin iyaka zuwa filin jiragen sama.