Jam’iyyar PDP ta kara jaddada cewa, dan takarar na shugaban kasar ta Atiku Abubakar ne a zahirance ya lashe zaben shekara ta 2023.
A cikin wata sanarwar da sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Debo Ologunagba ya fitar, ya caccaki ministan yada labarai Lai Mohammed game da furucin sa na baya-bayan nan.
Idan ba a manta ba, Lai Mohammed ya shawarci ‘yan adawar da ke kalubalantar sakamakon zaben shekara ta 2023 su rungumi kaddara kawai, inda PDP ta ce shugaba Buhari ya yi irin wannan tsokaci.
Jam’iyyar PDP, ta ce martanin Lai Mohammed ba komai ba ne illa tunzurawa irin ta jam’iyyar APC, domin ganin an zalunci jam’iyyun adawa a kotun zabe.
PDP ta kara da cewa, duk ‘yan Nijeriya su na sane cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zabe ba Tinubu ba, musamman idan aka yi la’akari da sakamakon da aka tattara daga rumfunan zabe.