Home Labaru Martani: Shari’ar El-Zakzaky Ba A Hannun Buhari Ta Ke Ba

Martani: Shari’ar El-Zakzaky Ba A Hannun Buhari Ta Ke Ba

879
0
Buhari
Buhari

Fadar Shugaban Kasa ta ce, shari’a ko tuhuma da kuma ci-gaba da tsarewar da ake yi wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ba laifin shugaban kasa ba ne.

Ta ce malamin ya na fuskantar tuhuma ne a Kaduna, don haka kada ma a dora wa gwamnati cewa ita ke da laifin ci-gaba da tsare shi.

Karanta Wannan: Tsare E-Lzakzaky: Sheikh Ahmad Gumi Ya Gana Da Bola Ahmed Tinubu

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Mabiya El-Zakzaky dai na ci-gaba da gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoran na su, kamar yadda kotu ta bada umarni a baya.

Garba Shehu, ya ce kamata ya yi ‘yan Shi’a su maida hankali a kan inda ake ci-gaba da shari’a, domin batun EDl-Zakzakky ya na kotu ba a hannun shugaban kasa ba.