Home Labaru Majalisar Dattawa Ta Bawa Buhari Wa’adin Kwanaki 5

Majalisar Dattawa Ta Bawa Buhari Wa’adin Kwanaki 5

302
0
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare

Majalisar dattawa ta ba shugaba Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki biyar ya mika mata sunayen mutanen da ya ke son nadawa ministoci.

Tun bayan rantsar da shi akalla watanni biyu da su ka gabata, amma har yanzu shugaba Buhari bai mika wa majalisar sunayen ministocin ba.

Majalisar dai ta bukashi shugaba Buhari ya gaggauta mika mata sunayen kafin ranar 26 ga watan Yuli, inda za ta fara hutu ta dawo ranar 26 ga watan Satumba.

Shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar dattawa Sanata Adedayo Adeyeye, ya ce majalisar za ta tafi hutun ta matukar fadar shugaban kasa ta gaza mika mata sunayen nan da ranar Juma’ar mako mai kamawa.