Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya yi watsi da jita-jitar da ke cewa ya na shirin barin jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Samuel Ortom ya shaida wa manema labarai cewa, babu wani dalilin da zai sa shi yin hakan, domin tun farko da shi aka gina jam’iyyar PDP, don haka babu abin da zai sa ya barta a yanzu.
Ya ce shi cikakken dan jam’iyar PDP ne, kuma ya na dauke da katin shedar zama dan jam’iyar, sannan a karkashin ta ne ya yi nasarar lashe zabe a karo na biyu.
Gwamnan ya kuma gargadi masu yada jita-jitar cewa ya ba gwamnan jihar Kogi shawara ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyar Accord.
Ya ce ba ya da masaniya a kan siyasar jihar Kogi, domin ya na fama ne kawai da da abin da ya shafi jihar Benue don ganin ya shawo kan matsalolin ta.