Home Labaru Albashi: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Sha Alwashin Fara Aiki Da Sabon Tsari

Albashi: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Sha Alwashin Fara Aiki Da Sabon Tsari

862
0

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta gama shiri tsaf domin biyan sabon tsarin albashin ma’aikata na naira dubu 30, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai, kwamishinan yada labara na jihar Ibrahim Umar Sade, ya ce gwamnan jihar Muhammad Abubakar ya ce a shirye ya ke ya fara biyan sabon albashin ga ma’aikatan jihar.

Sai dai ya ce bai san ko sabuwar gwamnati da za ta karbi mulki a hannun shi za ta iya ci-gaba da biyan sabon albashin ba.

Kwamishinan ya kara da cewa, damuwar gwamnan jihar a ko da yaushe ita ce biyan ma’aikata albashin su ba tare da sun biyo bashi ba.

Shugaban kungiyar kwadago ta jihar Bauchi Hashimu Muhammad, ya ce kungiyar ta na jin dadi da sabon karin albashin da gwamnatin tarayya ta kaddamar, don haka ba su ga dalilin da zai sa a ki fara biyan sabon albashin ba.

Leave a Reply