Home Labaru Kano: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Farautar Mutumin Da Ya Kashe Jami’inta

Kano: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Farautar Mutumin Da Ya Kashe Jami’inta

321
0

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta Jihar Kano ta ce ta fara aiki domin kamo wanda ya kashe Sufetan ‘Yan sanda, Isiyaku Babaji a gidansa da ke Sharada Quatrers.

 Ahmed  Illiyasu , Kwamishinan 'Yan sanda, A Jihar Kano
Ahmed Illiyasu , Kwamishinan ‘Yan sanda Na Jihar Kano

Kwamishinan ‘Yan sanda, na jihar Ahmed Illiyasu ne ya tabbatar da mutuwar sufetan,  duk da cewa bai bayar da bayanai masu yawa ba, ya ce an kama mutane da dama da ake zargi da hannu cikin kisar dan sandan duk da cewar suna bin sahun wanda ya yi kisar.

Karanta Wannan: Kisar ‘Yan Sanda 3: Jami’an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya A Ibbi, Na Taraba

Ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama suna amsa tambayoyi a sashin kula da manyan laifuka na rundunar.

Kwamishina Illiyasu, ya kuma gabatar da wasu mutane 116 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar da suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa  da satar mota da sauransu.

Cikin wadanda aka kama har da wani da ake zargi da kashe wata yarinyar ‘yar shekara 8 da aka sace ta yayin da ta ke hanyar komawa gida daga islamiyya tare da ‘yan uwanta a unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Nasarawa na jihar Kano.