Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum 670 da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar.
Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas ce ta fi yawan mutane inda ta ke da 277.
Korona ta kuma kama mutum 199 a Kaduna daga farkon Janairu zuwa ranar Litinin.
A babban birnin tarayya Abuja mutum 120, sai Kwara mai mutum 20 yayin da Abia ke da 14.
A Katsina da Gombe mutum tara tara cutar ta kama a jihohin, a Bauchi mutum shida
Yawan masu kamuwa da cutar na ƙaruwa a Najeriya, tun bayan ɓullar sabon nau’in cutar korona na Omicron a ƙasar nan.
You must log in to post a comment.