Gwamnatin Tarayya ta karyata jita-jitar da ake watsawa cewa za a janye tallafin man fetur.
Ministar Kudi Zainab Ahmed ta bayyana haka, biyo bayan ganawar ta da masu zuba jari da shugabannin Bankin Bada Lamuni na Duniya da kuma Bankin Duniya a Birnin Washington DC na kasar Amurka.
Ministar ta bayyana haka ne a matsayin martani dangane da shawarar da Asusun bada lamuni ya ba Nijeriya, cewa idan ta na so ta tsira da mutuncin ta sai ta cire tallafin man fetur.
Wannan ya sa masu motoci da sauran ababen hawa su ka shiga rudun bin layin sayen man fetur don gudun kada a kara farashi a lokaci daya, yayin da masu gidajen mai sun rika kulle wasu gidajen mai a tunanin za a yi kari don su saida na su da tsada.
Ministar ta cigaba da cewa, babu wani shiri nan kusa ko zuwa gaba da gwamnatin tarayya ke yi da nufin janye tallafin man fetur.