Home Labaru Rikicin Zamfara: Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Ta’adda Rubdugu A Kauyen Tsanau

Rikicin Zamfara: Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Ta’adda Rubdugu A Kauyen Tsanau

871
0

Rahotanni na cewa, Sojoji sun yi wa mahara kisan rubdugu a kauyen Tsanau da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce, sojojin sun kewaye maharan da misalin karfe 1 na rana, inda su ka datse duk wata hanyar shiga da fita kafin su fara afka wa maharan.

Wata majiya ta ce, yayin da wasu sojojin su ka tare hanyar shiga da fita daga garin, wasu kuma sun kutsa cikin kasuwar kauyen su ka darkaki maharan da ke yawon su kai tsaye a cikin kasuwar dauke da bindigogi.

Majiyar ta ce, sojojin sun kashe mahara da dama, wasu kuma sun jefar da bindigogin su su ka ranta a na kare, ganin yadda sojoji ke ta ratattaka masu wuta.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa, lokacin da sojojin su ka je ba su sha wahalar shaida maharan ba, saboda dukkan su su na yawon su kai tsaye dauke da bindigogi.

Kakakin Yada Labarai na Sojojin Zamfara Clement Abiade, ya tabbatar da rahoton kashe maharan, kuma ya ce har yanzu ana ci-gaba da darkakar su ana kashewa.