Home Labarai Harin Jirgi: Dangin Wadanda Aka Sace Sun Ba Gwamnati Sa’o’i 72 Ta...

Harin Jirgi: Dangin Wadanda Aka Sace Sun Ba Gwamnati Sa’o’i 72 Ta Dauki Mataki

44
0

Kwanaki goma sha biyar da kai harin jirgin kasa a hanyar Abuja
zuwa Kaduna, ‘yan’uwan mutanen da aka sace sun ce, lokaci ya
yi da ya kamata gwamnati ta sama ma wadanda aka kama mafita tunda ‘yan bindiga sun ce da gwamnati za su yi Magana.

Sauya sabon salon sakin faya-fayan bidiyo masu dauke da
wadanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan dai ya tada
hankalin ‘yan’uwan mutanen da aka sace, har wasu daga cikin
su na ba gwamnati wa’adin sa’o’i 72 ta dauki matakin karbo
‘yan’uwan su ko kuma su shiga dajin da kan su.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-rufa’i ya garzaya fadar
shugaban kasa game da matsalar tsaro, kuma tun a lokacin ya
sanar da cewa akwai alamun sai gwamnati ta sa baki.

Maganar sulhu da ‘yan bindiga dai na daga cikin abubuwan da
wasu ke ta kwadaitarwa, lamarin da Sheikh Ahmad Gumi ya ce
ita ce babbar mafita.

Yanzu haka dai akalla faya-fayan bidiyo uku ke nan ‘yan
bindigar su ka fitar, kuma a ciki ne su ke jaddada cewa
gwamnati ta san abin da su ke nema.