Home Labaru Martani: Kungiyar Dalibai Ta Najeriya Tarufe Kamfanin Mtn A...

Martani: Kungiyar Dalibai Ta Najeriya Tarufe Kamfanin Mtn A Kaduna

374
0

Kungiyar Dalibai ta  Najeriya ta rufe kamfanin sadarwa na MTN mallakin kasar Afirka ta Kudu a Kaduna a sakamakon kisan gillan da aka yi wa ‘yan Najeriya 118 a kasar a shekaru biyu da suka gabata.

Daraktan kungiyar mai kula da tafiye-tafiye, Dominic Philip ya bayyana hakan, inda ya ce  hakan ya zama wajibi domin kawo karshen kisan wulakancin da ake yi wa mutanen kasashen Afirka musamman Najeriya a kasar Afirka ta Kudu.

National Association Of Nigerian Students

Philip,  ya bayyana irin gudumuwar da Najeriya ta ba kasar Afirka ta Kudun lokacin da take fafutukar neman ‘yancin kanta daga hannun turawan mulkin mallaka amma duk da haka ake kashe ‘yan Najeriya.

Daraktan ya ce sauran kasashen Afirka sun taka mahimmiyar rawa wajen nemawa bakaken fata ‘yanci a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 1994 inda ya ce Najeriya ce kan gaba.

Ya ce bayyana mamakinsa a fili cewa cikin mutum 118 da aka kashe a kasar Afrika ta Kudu , 13 daga cikinsu jami’an yan sanda ne suka kashesu.

Daga  karshe ya yi kira a madadin kungiyar dalibai Ta najeriya wato NANS, ta rufe duk wani kamfanin Afirka ta Kudu dake Najeriya a dalilin kisa na ba gaira ba dalilin da suke yi wa yan Najeriya.