Home Labaru Martani: Kudin Mazabu Ba Aljihun ‘Yan Majalisa Su Ke Zuwa Ba –...

Martani: Kudin Mazabu Ba Aljihun ‘Yan Majalisa Su Ke Zuwa Ba – Shekarau

287
0
Martani: Kudin Mazabu Ba Aljihun ‘Yan Majalisa Su Ke Zuwa Ba - Shekarau
Martani: Kudin Mazabu Ba Aljihun ‘Yan Majalisa Su Ke Zuwa Ba - Shekarau

Dan majalisar dattawa Sanata Ibrahim Shekarau, ya bukaci a kara yawan kudin ayyukan mazabu da ake ba ‘yan majalisun dokoki na tarayya.

Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce kudaden da ake ba su domin aiwatar da ayyukan yankunan da su ke wakilta ba su taka kara sun karya ba, don haka ne ba a ganin tasirin ayyukan.

A cewar sa, wasu ‘yan Nijeriya na da tunanin cewa kudin su na zuwa aljihun ‘yan majalisar ne, ba tare da fahimtar cewa aikin su shi ne bin sawun kudin don tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan da aka tsara yi da su ba.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samar da wata hanya da za a rika bibiyar ayyukan da aka tsara yi don ganin an aiwatar da su ko akasin haka.

Ibrahim Shekarau, ya kuma musanta kallon da ake yi wa ‘yan majalisa a matsayin ‘yan amshin shata, inda ake zargin su da amincewa da bukatun bangaren zartarwa ba tare da bin diddigi ba musamman kan abin da ya shafi kasafin kudi.