Home Labaru Ilimi Martani: Hukumar JAMB Ta Karyata Zargin Cire Wa Dalibai Maki Dari-Dari

Martani: Hukumar JAMB Ta Karyata Zargin Cire Wa Dalibai Maki Dari-Dari

307
0

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’o’i JAMB, ta karyata rade-radin da ke cewa za ta rage maki dari-dari da daliban da su ka zana jarabawar su ka samu.

Hakan kuwa ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Fabian Benjamin ya fitar.

Rahotanni sun ce, hukumar ta dauki aniyar rage maki dari daga cikin abin da wasu dalibai su ka samu, matukar aka same su da laifin satar jarabawa.

Hukumar ta gargadi dalibai da iyaye su guji shiga hannun ‘yan damfara da ke neman a ba su kudi da sunan za su tallafa wa daliban su samu makin da ake bukata.

Idan dai za a iya tunawa, a wata tattaunawa da Benjamin ya yi da manema labarai, ya gargadi dalibai su guji jita-jitar da ake yadawa a shafukkan sada zumunta na zamani.