Wasu gungun ‘yan bindiga sun bude wa mazauna kauyen Sherere da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma tare da raunata wasu da dama.
‘Yan bindigar dai sun afka wa kauyen ne a kan manyan Babura, inda su ka shiga harbin kan-mai-uwa-da-wabi, daga bisani su ka bi duk wasu shaguna da ababen hawa su na banka masu wuta.
Wani mazaunin kauyen Dikko Shere ya shaida wa manema labarai cewa, sai da ta kai ga sun kasa fita daga gidajen su domin gudanar da jana’izar wadanda ‘yan bindigar su ka kashe.
A yan kwanakin nan dai, matsalar hare-haren ‘yan bindiga ta yi kamari a jihar Katsina, inda ko a makonni biyu da su ka gabata, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsamiyar Jino su ka kashe mutane da dama.