Dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya gargadi masu yawon bude ido su kiyayi ziyartar jihar Kaduna.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, bayan kisan wata ‘yar kasar Birtaniya da wata kwararriya a fannin sadarwa na kamfanin Mercy Corps da sauran matafiya a garin Kajuru na jihar Kaduna.
Sanatan, ya ce jihar Kaduna ba ta da tsaro ga masu yawon bude ido, ya na mai cewa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba su dauki lamarin su da wasa ba.
Yayin da ya ke Allah-wadai da kisan, Shehu Sani ya mika jajen sa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ya na mai cewa ana samun tashin hankali ne idan gwamnati ta gaza aiwatar da aikin ta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ko kuma idan tsarin ta ya gaza.