Home Labaru Martani: Gwamnatin Ta Fara Magana Da Boko Haram Don Ceto Ma’aikatan Agaji’

Martani: Gwamnatin Ta Fara Magana Da Boko Haram Don Ceto Ma’aikatan Agaji’

308
0

Gwamnatin tarayya ta  fara tattaunawa da Boko Haram kan wani yunkurin kubutar da Leah Sharibu da sauran wadanda kungiyar ake garkuwa da su.

Wannan ya biyo bayan wani bidiyo da ya bulla na wasu ma’aikatan agaji, inda wata mace daga ciki ta roki mahukuntan Najeriya da kasashen duniya da su taimaka wajen ganin an kubutar da su.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce ya na fatan za a kubutar su ta hanyar tattaunawar da ake yi., amma bai yi wani karin haske ba, game da batun tattaunawar, kodayake ya bukaci masu garkuwar da su tausaya.

Garba Shehu, ya ce tattaunawar ba iya wadannan ta shafa ba, “har da Leah Sharibu” wadda ta na daya daga cikin ‘yan mata ‘yan makaranta da Boko Haram ta sace daga garin Dapchi na jihar Yobe a watan Maris na 2018.

Sannan kuma bai fadi cewa ko Leah Sharibu ta na raye ba, amma ya ce fadar shugaban kasa za ta dauki mataki, bayan tunanin da ake cewa an kashe dalibar.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu

Ma’aikatan agajin wadanda suke aiki da wata kungiyar bayar da agaji ta kasar Faransa mai suna Action Against Hunger, an sace su ne a jihar Borno.