Home Labaru Ta Kacame Tsakanin Atiku Da Buhari A Kan Hana ‘Yan Siyasa Shiga...

Ta Kacame Tsakanin Atiku Da Buhari A Kan Hana ‘Yan Siyasa Shiga Amurka

1023
0

Hukuncin da kasar Amurka ta yanke na hana wasu ‘yan siyasa shiga kasar bisa zargin su da hannu a yunkurin tauye dimokradiyyar Nijeriya a zaben shekara ta 2019, ya haddasa musayar kalamai tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.

Yayin da Atiku ke kallon yunkurin a matsayin tabbacin an yi magudi a zaben Shugaban kasa da ya gabata, kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari da Osinbajo kuma na kallon hukuncin a matsayin wanzar da shaharar Shugaba Buhari a kasashen duniya.

Atiku Abubakar, ya ce takunkunmin hana shiga kasar Amurka da aka kakaba wa wasu ‘yan siyasar Nijeriya da su ka kawo cikas a zaben da ya gabata, alama ce da ke tabbatar da cewa an tafka magudi.

Sai dai kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari da Osinbajo cewa ta yi, takunkumin da gwamnatin Amurka ta sa a kan wasu rukunin ‘yan siyasar Nijeriya, alama ce da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu karbuwa kuma ya shahara a tsakanin kasashen duniya.

Leave a Reply