Home Labaru Garkuwa Da Mutane: An Sace Ma’aikaciyar Kotu A Kaduna

Garkuwa Da Mutane: An Sace Ma’aikaciyar Kotu A Kaduna

565
0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da sace Darektar kotun daukaka kara Hajiya Aishatu Muhammad tare da kashe dan ta.

Mai  magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya ce  ‘yan bindigar da suka sace ta, sun kashe dan ta a harin da suka kai kuma an sanar da rundunar faruwar lamarin.

Ya ce ofishin rundunar  ‘yan sanda  dake  Sabon-Tasha ne ya sanar da shelkwatar ‘yan sanda cewa ‘yan bindiga sun shiga gidan wani mutum mai suna Hussain Manjalo a garin Doka Mai Jama’a, karamar hukumar Chikun, inda suka harbe dansa a yayin da yake kokarin hana su garkuwa da mahaifiyar sa.

Hajiya Aisha Muhammad wanda a Kayi Garkuwa Da Ita

Ya ce ‘yan bindihar sun sace mahaifiyar yaron da suka kashe Hajiya Aishatu Muhammad, wadda ita ce darekta a kotun daukaka kara ta jihar Kaduna.

Ya ce, rundunar ‘yan sanda ta aika jami’anta ba tare da bata lokaci ba,  domin su dauko gawar wanda aka kashe domin kai ta asibiti. Daga karshe ya kara da cewar an kara tura wata runduna da ta hada da jami’an ‘yan sandan sashen yaki da garkuwa da mutane domin kubutar da matar tare da kama masu laifin