Home Labaru Martani: Ban Ce Dole A Ba Yankin Kudu Maso Yamma Mulki A...

Martani: Ban Ce Dole A Ba Yankin Kudu Maso Yamma Mulki A 2023 Ba – Sanata Lawan

290
0

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya karyata zargin abin da ya kira ji-ta-ji-tar kafar sada zumunta ta yanar gizo, cewa ya fara yi wa Yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya fafutukar karbar shugabancin Nijeriya a shekara ta 2013.

Wani rahoto da aka rika watsawa da sunan Sanatan, ya nuna ya na goyon bayan a ba yankin Kudu Maso Yammancin Nijeriya mulki a shekara ta2023 domin a karrama marigayi Mashood Abiola, sai dai Sanatan ya musanta wannan labara.

Ya ce an yi furucin, amma ba shi ne ya yi ba, wani mai irin sunan sa ne kuma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Adamawa.

Sanatan ya kara da cewa, an ja hankalin sa game da wani furuci da ke yawo a kafafen yada labarai, inda aka ce ya ce dole a mika mulki ga Shiyyar Kudu maso Yammacin Nijeriya a shekara ta 2023.

Leave a Reply