Home Labaru Zaben 2019: Yadda Tulin Jam’iyyu Barkatai Su Ka Dagula Mana Sha’ani –...

Zaben 2019: Yadda Tulin Jam’iyyu Barkatai Su Ka Dagula Mana Sha’ani – INEC

366
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce yawan jam’iyyu 91 da aka yi wa rajista su ka kuma shiga zabe ya kawo mata cikas tare da haifar da matsaloli wajen gudanar da ayyukan ta.

Kwamishinan Zabe mai Kula da Jihohin Kwara da Kogi da Nasarawa Mohammed Haruna ya bayyana haka, a wajen wani taro da aka tattauna yadda aka gudanar da zabubbukan shekara ta 2019 da ya gudana a jihar Kwara, inda ya ce yanzu haka akwai kararraki 700 daga sassa daban-daban na Nijeriya.

Ya ce akwai wasu kararraki sama da 800 da ake kalubalantar sakamakon zabubbukan fidda-gwanin da jam’iyyu su ka gudanar.

A karshe ya ce akwai bukatar duba yawan wadannan jam’iyyu, domin jama’a sun fara kukar cewa jam’iyyu 93 sun yi matukar yawa, domin yawan jam’iyyu 73 da su ka shiga zaben shugaban kasa ne babbar matsalar da ta fara afka wa hukumar zabe.

Leave a Reply