Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya hada gwiwa da gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Nijeriya domin magance masalar hare-haren ‘yan bindiga.
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro na tarayya da na jihohi su fara aiwatar da tsare-tsaren su na samar da tsaro.
Wannan dai ya na zuwa ne, bayan harin da aka kaddamar a Tungar Kafau da Gidan Wawa da ke karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda akalla mutane 34 su ka rasa rayukan su.
Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, gwamnatin sa ta maida hankalin a kan aikin da ya rataya a wuyan ta, na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai cewa gwamnati ba za ta gaza ba a wannan bangaren.