Home Labaru Kasuwanci Martani: Babu Shirin Maida Asusun Ajiyar Kudaden Waje Zuwa Na Naira –...

Martani: Babu Shirin Maida Asusun Ajiyar Kudaden Waje Zuwa Na Naira – CBN

10
0

Babban bankin Nijeriya CBN, ya musanta rahotannin da ke cewa ya umurci bankuna su maida asusun ajiyar abokan huldar su na kudaden kasashen waje zuwa na Naira.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, daraktan yada labarai na bankin Osita Nwanisobi, ya ce babu gaskiya a wannan ikirarin, hasali ma sanarwar da ake yadawa game da haka karya ce tsagwaron ta.
Bankin ya sake yin tuni da cewa, ya sha bada tabbacin cewa babu wani shirn maida asusun ajiyar kudaden kasashen waje zuwa na Naira, don kawai ya na so ya magance karancin dalar Amurka.
A karshe bankin ya ja kunnen kamfanoni da daidaikun mutane game da amfani da hatimi ko alamar bankin, ya na mai cewa ya sanar da hukumomi kuma duk wanda aka kama zai dandana kudar sa.