Home Labaru Bincike: Sama Da Muggan Makamai Dubu 60 Na Hannun ‘Yan Bindiga A...

Bincike: Sama Da Muggan Makamai Dubu 60 Na Hannun ‘Yan Bindiga A Arewacin Nijeriya

188
0

Wani rahoton bincike ya ce, adadin muggan makaman da ke hannun ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane a yankin arewa maso yammacin Nijeriya sun zarta dubu 60.

Malami a sashen nazirin tarihi na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto Dakta Muratala Ahmed Rufa’i ya bayyana haka, a cikin wani binciken da ya shafe akalla shekaru 10 ya na yi a kan matsalar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Binciken, ya ce tuni matsalar tsaro ta zame ma wasu ciki har da ‘yan bindigar hanyar samun kudade saboda safarar makamai da su ke yi.

Dangane da kudaden da ake samu daga safarar makaman kuwa, binciken ya ce ‘yan bindigar su na amfani da su wajen sayen miyagun kwayoyi da Caca da wayoyin hannu da neman mata da sauran bukatu.

Dakta Murtala Rufa’i, ya ce ya samu bayanan binciken sa ne daga hirarrakin da ya samu damar yi da wasu daga cikin ‘yan bindigar, da wasu mutanen da tashin hankalin ya shafa.

Leave a Reply