Home Labaru Jiki-Magayi: ‘Yan Bindiga Sun Shiga Rudani Sakamakon Matakan Hukumomi

Jiki-Magayi: ‘Yan Bindiga Sun Shiga Rudani Sakamakon Matakan Hukumomi

97
0

Matakan da aka dauka domin dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar Zamfara da jihohi makwafta sun fara tasiri, wanda yanzu haka rahotanni ke nuni da cewa maharani sun shiga rudani sakamakon rashin man fetur da sauran mahimman abubuwan bukatar su.

A makon da ya gabata ne, jihohin Zamfara da Katsina da Neja da Kaduna su ka ayyana dokar haramta saida man fetur a jarka da kuma cinikin shanu tare da rufe kasuwannin mako-mako da zummar taka wa ‘yan ta’addan birki.

Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun shiga mawuyacin hali na yunwa da rashin mahimman abubuwan bukata, har ta kai ga yanzu su na karbar shinkafa da taliya a matsayin abin fansa.