Home Labaru Kungiyar Afenifer Ta Ce Ana Nuna Wa Osinbajo Wariya A Gwamnatin Buhari

Kungiyar Afenifer Ta Ce Ana Nuna Wa Osinbajo Wariya A Gwamnatin Buhari

283
0
Kungiyar Yarbawa Ta Afenifere

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere, ta yi zargin cewa ana maida mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo saniyar-ware a tafiyar da al’amuran ƙasa.

Afenifere ta yi zargin ne, biyo bayan ɗaukar dokar hana haƙar mai da shugaban ma’aikata Abba Kyari ya yi har zuwa birnin London ya kai wa Shugaba Buhariya ya sanya mata hannu.

Yarbawa dai na kallon lamarin a matsayin ƙoƙarin maida Osinbajo saniyar-ware, musamman a kan matakin ƙin miƙa ma shi ragamar mulki.

Kungiyar ta shaida wa manema labarai cewa, in dai har sai shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya ɗauki takardu zuwa London ya kai wa shugaban ƙasa domin ya sa masu hannu, to hakan ya na nufin an fitar da Osinbajo daga hidimar gwamnati kenan.

Wani lauya Barista Al-Zubair Abubakar, ya ce Shugaba Buhari bai saba doka ba don ya sa hannu a kan sabuwar dokar hakar mai da majalisar dokoki ta ƙasar ta amince da ita yayin da ya ke ziyara a Burtaniya.