Home Labaru Martani: Ba Zan Bada Hakuri Don Na Kira Buhari Mai Kyakkyawar Zuciya...

Martani: Ba Zan Bada Hakuri Don Na Kira Buhari Mai Kyakkyawar Zuciya Ba – Umahi

16
0

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ce babu dalilin da zai sa ya bada hakuri don ya kira shugaba Buhari a matsayin mutum mai kyakkyawar zuciya, kuma uba.

Umahi ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi baƙuncin tsohon shugaban jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff a gidan gwamnatin jihar da ke Abakiliki.

Gwamnan ya jaddada cewa, ba ya wani da-na-sani a kan kalaman sa, kuma babu wata sukar mutane da za ta sauya ma shi ra’ayi.

Dave Umahi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su cigaba da goyon bayan shugaba Buhari, domin mutum ne ɗaya tilo da ya fita daban da saura ta fuskar nagarta.