‘Yan majalisar tarayya na yankin kudancin Nijeriya, sun kafa kwamiti da zai lalubo hanyoyin ceto shugaban kungiyar masu neman kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Bayanin haka ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ‘yan majalisar su ka fitar, jim kadan bayan sun gudanar da taro a gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu.
Sanarwar, mai dauke da sa hannun dukkan ‘yan majalisar, ta ce an yi taron ne domin tattaunawa a kan batun Nnamdi Kanu da yadda za a warware matsalar shi.
‘Yan majalisar, sun kuma yi Allah-Wadai da asarar rayyuka da dukiyoyi da hana rubuta jarrabawa a makarantun yankunan kudu maso gabas da sunan tilasta zaman gida da kungiyar IPOB ke yi.














































