Home Labaru Martani: Atiku Abubakar Ya Bayyana Hukumar EFCC A Matsayin Karen-Farauta

Martani: Atiku Abubakar Ya Bayyana Hukumar EFCC A Matsayin Karen-Farauta

231
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya maida martani game da naira miliyan 50 da hukumar EFCC ta gano a dakin karatu na Obasanjo da ta ce mallakin surukin sa Babalele Abdullahi ne.

Atiku Abubakar ya maida martanin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana hukumar EFCC a matsayin Karen-farautar gwamnatin APC da shugaba Muhammadu Buhari.

Ya kuma kara bayyana hukumar EFCC a matsayin wani sashe na watsa farfagandar jam’iyyar APC, sai dai ya ce babu wata barazana da za ta sa Obasanjo ya yi shiru da bakin sa matukar ya na ganin ana sukuwa a kan ‘yan Nijeriya.

Ya ce rahoton da EFCC ke watsawa game da naira miliyan 50 da ta ce ta gano a dakin karatun Obasanjo cewa mallakin Abdullahi Babale ne, ta na yi ne kawai domin haddasa rikici tsakanin shi da Obasanjo.

Atiku ya kuma bada tabbacin cewa, Babalele Abdullahi bai taba ba dakin karatu na Obasanjo kudi ba, abin da su ka sani kawai shi ne, ya kai wanda ya ba cibiyar tallafin naira miliyan 50 kamar yadda sauran mutane su ka yi.