Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kone Motocin Sojoji A Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Kone Motocin Sojoji A Jihar Katsina

362
0
'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kone motocin sojoji uku, yayin wata arangama da su ka yi da tawagar jami’an tsaro a kan hanyar zuwa Shimfida daga karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Mata uku dai sun samu raunuka yayin musayar wutar, kamar yadda wata majiyar ‘yan sanda a jihar Katsina ta sanar.

Rahotanni sun ce ‘yan bidigar sun kai hari tare da rufe hanyar da tsakar, inda kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ya ce rufe hanyar da maharan su ka yi ne ya janyo musayar wuta tsakanin su da jami’an tsaro.

Ya ce sakamakon musayar wutar da aka yi ne, ‘yan bindigar su ka kone motocin sojoji uku da ta jami’an tsaro na Civil Defence guda daya, yayin da lamarin ya rutsa da wata motar fasinjoji dauke da ‘yan kasuwa zuwa Shimfida.