Home Labaru Safarar Kwayoyi: An Yanke Wa ‘Yan Nijeriya 23 Hukuncin Kisa A Saudiyya

Safarar Kwayoyi: An Yanke Wa ‘Yan Nijeriya 23 Hukuncin Kisa A Saudiyya

418
0

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi da haramtattun kayyaki a kasar Saudiyya, ta yanke wa akalla mutane 23 ‘yan Nijeriya hukuncin kisa.

An dai kama mutanen ne da tulin kwayoyi a cikin cikunan su bayan sun hadiye, lamarin da ya saba wa dokokin kasar.

Wata majiya ta ce an kama mutanen ne tsakanin shekara ta 2016 da 2017 a filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jiddah, da kuma filin jirgin sama na Yarima Muhammad bin Abdu-Aziz da ke birnin Madinah, bayan an same su dauke da haramtattun kayayyaki.

Hakan dai ya na zuwa ne, makonni kadan bayan hukumomin Saudiyya sun hukunta Kudirat Afolabi bisa safarar migayun kwayoyin da wani dan Nijeriya Saheed Sobade, wanda aka kama da hodar iblis mai nauyin kilo 1,183 a Jiddah.

Leave a Reply