Home Labarai Mamakon Ruwan Sama Ya Sanadiyyar Mutuwar Mutane 6 Tare A Jihar Jigawa

Mamakon Ruwan Sama Ya Sanadiyyar Mutuwar Mutane 6 Tare A Jihar Jigawa

315
0

Akalla mutane shida sun rasa rayukan su, yayin da wasu da dama su ka jikkata sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi a karamar hukumar Kafin-Hausa ta jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar Muhammad Saminu ya bayyana haka, lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan wasu da lamarin ya shafa.

Muhammad Saminu, ya ce mutane 6 ne suka mutu, yayin da wasu 60 su ka samu raunuka tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Wani mazaunin garin ya ce, guguwar ruwan sama da ta afku a daren Talata, ta sa daruruwan iyalai sun rasa matsugunan su, lamarin ya tilasta masu samun mafaka a gidajen jama’a da gidajen ‘yan’uwa.

Leave a Reply