Home Labarai Kankwaso Ya Zabi Fasto Matsayin Mataimaki A Zaben 2023

Kankwaso Ya Zabi Fasto Matsayin Mataimaki A Zaben 2023

14
0

Jam’iyyar NNPP, ta ce dan takarar ta na shugaban kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zabi Bishop Isaac Idahosa daga jihar Edo a matsayin abokin takarar sa a zaben shekara ta 2023.

Bishop Isaac Idahosa dai babban Fasto ne a cocin God First Ministry da ke da helkwata a jihar Legas.

Zaben faston dai ya na zuwa ne, bayan rade-radin da ke cewa Kwankwaso ya na neman zaben tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi a matsayin abokin takarar sa.