Home Labarai An Bayyana Dangantakar Sin Da Afrika A Matsayin Mai Gagarumar Tasiri

An Bayyana Dangantakar Sin Da Afrika A Matsayin Mai Gagarumar Tasiri

89
0

Daraktan cibiyar nazarin kasar Sin da ke Nijeriya Charles Onunaiju, ya bayyana dangantakar Sin da Afrika a matsayin mafi tasiri a duniya, saboda muhimmancin ta wajen bada gudunmuwa ga sauyin yanayin nahiyar.

Ya ce duk da cewa ana gudanar da dangantakar ne bisa gaskiya da adalci, amma kafafen yada labarai na yamma su na neman duk wata kafa ta sukar ta tare da bata mata suna.

Charles Onunaiju ya kara da bada misali da wani shirin bidiyo da wata kafar yada labarai ta fitar a baya bayan nan, wadda ke nufin amfani da wariyar launi wajen samun kudi, a matsayin wanda ya yi matukar shafa wa dangantakar bangarorin biyu bakin fenti.

Leave a Reply