Home Labaru Neman Mafita: Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Tsaron Najeriya

Neman Mafita: Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Tsaron Najeriya

18
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganarwar sirri da shugabannin tsaron Najeriya a fadarsa da ke nan babban birnin tarayya a Abuja.


Tattaunawar wadda aka fara da misalin karfe 10 na safe, ta samu
halartar mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da sakataren
gwamnati Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan fadar
shugaban kasa Ibrahim Gambari.


Sauran sun hada da ministan tsaro Bashir Magashi da ministan
shari’a Abubakar Malami da ministan harkokin kasashen waje
Geoffrey Onyeama.