Ministan Shari’a kuma babban Lauyan Gwamnati, mai mukamin SAN Abubakar Malami, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewa cikin shekarar sa ta farko bayan karbar mulki a shekara 2015.
Abubakar Malami ya ce shugaba Buhari ya ceto Najeriya ne
yayin da take shirin rushewa sakamakon karyewar tattalin arziki
da sauran matsaloli cikin kankanin lokaci.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Rediyon
Kano, inda ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu mummunan
koma baya kafin zuwan Buhari a shekarar 2015.
Ya ce abin da shugaba Buhari ya cimma cikin kankanin lokaci
ko kasashen da suka ci gaba ba za su iya ba.
Abubakar Malami ya ce kafin zuwan shugaba Buhari, akwai
matsalolin tsaro da yawa, musamman a Arewa maso Gabas,
amma a yanzu an yi nasarar dakile hare-hare domin a yanzu a
kan shafe tsawon lokaci kafin aji an kai hari Kasuwanni, ko
wuraren ibada da dai sauran su.
Har wa yau, ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya da jami’an
tsaro ke aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen ayyukan ’yan
bindiga a Arewa maso yamma.














































