Home Labaru Jihohin Yammacin Amurka Na Cikin Duhun Rashin Lantarki

Jihohin Yammacin Amurka Na Cikin Duhun Rashin Lantarki

101
0

Kanƙara ta lulluɓe yankin yammacin Amurka, inda ta jefa dubbai cikin duhun rashin lantarki.

Kankara mai tudun inci 30 ne ta yi ta faɗowa a arewacin California cikin awa 24, hakan ya jawo ɗaukewar lantarki da kuma rufe Tituna.

A ranakun karshen mako ma, guguwa haɗe da ambaliyar ruwa ta afka wa kudancin Carlifornia, wadda ta lalata lantarki da kuma cika tituna da ruwa.

Hukumar yanayi ta ƙasa ta ce ruwan sama mai tudun inci 1.8 zai ci gaba da zubowa a Reno, da Navada daga Lahadi da dare zuwa Litinin din nan.

Leave a Reply