Home Labarai Gwamnati Za Ta Rufe Kamfanonin Bada Rancen Kudi Da Suka Saba Kai’da

Gwamnati Za Ta Rufe Kamfanonin Bada Rancen Kudi Da Suka Saba Kai’da

84
0

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Najeriya wato FCCPC ta ce kwamitin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya ta kafa domin magance tauye hakkin mabukata da rashin adalci a masana’antar ba da rancen kudi za ta rufe sana’o’in masu ba da rance ba bisa ka’ida ban an bada jumawa ba.

Babban jami’in hukumar ta FCCPC, Babatunde Irukera ne ya bayyana
hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya
wato NAN a nan Abuja.
Ya ce idan ana iya tunawa, a farkon watan Nuwamban shekarar nan ne
gwamnatin tarayya ta soma aikin duba wasu haramtattun ayuka da kuma
rashin adalci a cikin harkar bayar da lamuni na masana’antar ba da
rance, tare da kafa kwamitin hadin gwiwa don shawo kan lamarin.
Babatunde Irukera ya ce ana sa ran kwamitin da gwamnatin tarayya ta
kafa da ya karbi wasikun koke ta na’ura sama da 500 da bayanai game
da binciken, zai jagoranci kokarin magance wasu dabi’un da za su iya
haifar da rashin tabbas ga wasu masu ba da rance wadanda aka fi sani da
loan sharks a turance.
Ya ce kwamitin hadin gwiwar ya kunshi wakilai daga hukumar FCCPC,
da babban bankin Najeriya wato CBN, da hukumar yaki da cin Hanci da
rashawa wato EFCC, da hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya
wato NITDA da kuma hukumar kare hakkokin dan adam wato NHRC.

Babban jami’in hukumar ta FCCPC, ya ce kwamitin zai kuma rubuta
ka’idojin wucin gadi, wadanda ya zama wajibi kamfanonin bayar da
lamuni na kudi su bi.