Home Labaru Malaman Jami’a Sun Fara Yajin Aiki

Malaman Jami’a Sun Fara Yajin Aiki

379
0
# DaDumiDuminsa: MALAMAN JAMI’O’I SUN FARA YAJIN AIKI A NAJERIYA
# DaDumiDuminsa: MALAMAN JAMI’O’I SUN FARA YAJIN AIKI A NAJERIYA

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta fara yajin aiki har sai abin da hali ya yi.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce kungiyar ta tsunduma cikin yajin akin ne saboda rashin amincewa da tsarin albashi na IPPIS da rashin biyan bukatun mambobin kungiyar

Da yake jawabi a hedikwatar kungiyar da ke Abuja, Farfesa Ogunyemi ya zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawuran shekarar 2009 da ta yi wa malaman na magance matsalolin jami’o’in.

A ranar 9 ga watan Maris da muke ciki ne kungiyar ASUU ta fara shiga yajin aikin wucin gadi saboda rashin biyan bukatun nasu.