Home Labaru Kiwon Lafiya Aisha Buhari Ta Yi Wa Dan Atiku Addu’ar Samun Saukin Da Kamuwa...

Aisha Buhari Ta Yi Wa Dan Atiku Addu’ar Samun Saukin Da Kamuwa Da Cutar Corona

458
0
Aisha Buhari Ta Yi Wa Dan Atiku Addu’ar Samun Saukin Da Kamuwa Da Cutar Corona
Aisha Buhari Ta Yi Wa Dan Atiku Addu’ar Samun Saukin Da Kamuwa Da Cutar Corona

Uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari ta yi wa dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar addu’ar samun lafiya cikin gaggawa, sakamakon yadda gwaji ya nuna ya na dauke da cutar Corona.

Aisha Buhari ta aika sakon addu’ar ne zuwa ga Atiku ta shafin sa na Twitter, bayan ya bayyana cewa dan sa ya kamu da cutar.

Uwargidan shugaban kasa Buhari ta wallafa a shafin Twitter cewa, ina addu’a domin ganin ganin dan ka ya samu lafiya Amin.

Tun farko dai, Atiku Abubakar ya sanar da cewa, dan sa ya kamu da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronaviru, wanda ya wallafa a  shafin san a Twitter a ranar Lahadin ta da gabata.

A cewar Atiku Abubakar an garzaya da dan nasa zuwa asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a birnin Abuja domin yi masa magani, tare da cewa  ya sanar da hukumar kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya NCDCG, kuma tuni an kai shi asibiti domin yi masa magani.