Home Labaru Kiwon Lafiya Corona: A Karon Farko Buhari Ya Yi Jawabi Ga ‘Yan Nijeriya

Corona: A Karon Farko Buhari Ya Yi Jawabi Ga ‘Yan Nijeriya

667
0
Buhari Ya Bukaci A Yi Bincike A Kan Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala
Buhari Ya Bukaci A Yi Bincike A Kan Gobarar ‘Yan Gudun Hijira Da Ke Ngala

A karon farko shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Karin haske a kan matakan da gwamnatin sa ta ke dauka a kan yaduwar cutar Coronavarus.

Buhari ya yi jawabin ne a cikin wani gajeren bidiyo, inda ya ce gwamnatin sa na aiki tare ma’aikatar lafiya domin ganin an kare al’ummar Nijeriya daga kamuwa daga annobar corona.

Shugaban kasa Buhari ya kara da cewa, yanzu gwamnatin ta maida hankali  a kan yadda za a takaita yaduwanr wannan annoba, bisa haka ne ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su tabbatar sun kiyaye dukkanin hanyoyin kamuwa da cutar.

Idan dai ba a manta ba, yan Nijeriya da dama sun yi ta korafi a kan shurun da shugaban kasa ya yi, matakin da ya sa wasu ke zargin sa da nuna halin ko-in-kula a kan barkewar cutar a Nijeriya.

Masana na ganin jawabin na shugaban kasa zai bude idanun wasu daga da ke karyata batun bullar cutar tare da daukar matakan kare kai daga kamuwa da ita.