Home Labaru Makomar Fulani: Buhari Ya Yi Tir Da Umurnin Dattawan Arewa

Makomar Fulani: Buhari Ya Yi Tir Da Umurnin Dattawan Arewa

196
0
Shugaba Muhammadu-Buhari-2
Shugaba Muhammadu-Buhari-2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci a yi watsi da kiraye-kirayen da Kungiyar Dattawan Arewa ta yi cewa Fulanin da ke zama a kudancin Nijeriya su gaggauta komawa Arewa.

Buhari ya ce kowace kabila na da damar zama inda ran ta ya kwanta mata ko da ba yankin ne asalin ta ba.

Ya ce kamar yadda Dokar Nijeriya ta shimfida, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare dukkan al’ummar Nijeriya a duk inda su ka samu kan su da zama.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya tambayi dalilin da zai sa irin wadannan dattawa masu kiran kan su shugabanni za su yi azarbabin shiga maganar da bai kamata su shiga su na bada gurguwar shawara ba.

Garba Shehu, Mai magana da yawun bakin shugaban kasa

Ya ce dattawan Arewa da sauran masu kiran kan su shugabannin kungiyoyi duk su na maganganun ne domin neman suna, ya na mai cewa sun dade su na bata sha’anin zamantakewar siyasar Nijeriya.

Shugaba Buhari, ya ce kada a sake a ba su kofar da za su rika karkatar da jama’a, musamman Fulani makiyaya da su ke kokarin yi wa romon-baka. �