Home Labaru Kiwon Lafiya Zakzaky Ya Nemi Kotu Ta Ba Shi Damar Zuwa Jinya

Zakzaky Ya Nemi Kotu Ta Ba Shi Damar Zuwa Jinya

604
0
Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Mabiya Akidar Shi’a Na Nijeriya
Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Mabiya Akidar Shi’a Na Nijeriya

Shugaban kungiyar mabiya akidar shi’a na Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinatu, sun nemi babbar kotun jihar Kaduna ta ba su izinin zuwa kasar India domin duba lafiyar su da su ka ce ta na tabarbarewa.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta na tuhumar Zakzaky ne a gaban kotu, bisa laifuffukan da su ka shafi kisan kai, da taro ba bisa ka’ida ba, da tada hankulan jama’a da kuma sauran laifuffuka da dama.

Wata kwakkwarar majiya ta ambato daraktan shigar da kara na gwamnatin jihar Kaduna Dari Bayero, ya na cewa a ranar Alhamis ne Alkali D.H Khobo zai cigaba da sauraren karar.

Bayero ya bayyana wa manema labarai cewa, El-Zakzaky ya mika wa kotu bukatar sa ne a ranar Larabar nan, inda ya nemi ta ba shi damar zuwa Asibitin Metanta da ke birnin New Delhi a kasar Indiya domin duba lafiyar sa, ya na mai alkawarin dawowa Nijeriya don ci-gaba da shari’a da zarar an sallame shi.